Mun samu labari cewa yanzu haka ana shirin cigaba da shari'a da Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki a babban Kotun Tarayya da ke Birnin Tarayya Abuja.
Labari ya zo mana daga Jaridar Daily Trust cewa a makon gobe ne za a kara zama a Kotu da Bukola Saraki inda 'Dan takarar PDP Abdurrahman Abdulrazaq ke kalubalantar zaben Bukola Saraki a matsayin Sanatan Jihar Kwara ta tsakiya.
A farkon makon nan ne Kotu ta sanar da Shugaban Majalisar da kuma Hukumar INEC game da wannan shari'a.
Abdulrazaq wanda yayi takarar karkashin PDP ya nemi Kotu ta hukunta Jami'an INEC da kuma Wakilan Saraki da APC a zaben.
Lauyan da ke kare 'Dan takarar PDP Sambo Muritala yana karar cewa an yi muna-muna a wasu wurare a Yankin ihar Kwara lokacin zaben inda yace Wakilan Bukola Saraki da Hukumar INEC sun sabawa ka'idojin zaben da aka gudanar a 2015.
Source :naij hausa
Title :
Bukola Saraki Zai Iya Rasa Kujerarsa A Majalisar Dattawa
Description : Mun samu labari cewa yanzu haka ana shirin cigaba da shari'a da Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki a babban Kotun Tarayya da ke Bi...
Rating :
5