Makwanni biyu bayan sace 'yan matan makarantar Dapchi 110 a jihar Yobe, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce zai kai ziyara a yankin domin ganawa da iyayen daliban.
A wata sanarwa da kakakin shugaban kasar Femi Adeshina ya sanyawa hannu, ya ce Buhari zai kuma ziyarci jihohin da suka yi fama da kashe kashe da suka hada da Benue da Taraba da Zamfara.
Sanarwar ta ce Buhari ya yanke shawarar kai ziyara yankunan ne bayan nazari kan rahoton da ya karba wanda Sojoji da jami'an tsaro suka tattara game da rikice-rikicen.
Sai dai wasu 'yan aksar da dama na ganin cewa shugaban ya yanke shawarar kai wadannan ziyarce-ziyarce ne saboda irin korafi da kuma kiraye-kirayen da aka yi ta masa na nuna masa muhimmanci ziyarar, musamman ma dai bayan da ya halarci daurin auren diyar Gwamna Abdullahi umar Ganduje na Kano a ranar Asabar din da ta gabata.
Daga yau ranar Litinin 5 ga watan Maris, shugaban zai fara kai ziyara jihar Taraba, kafin ya zarce zuwa Benue da Yobe da Zamfara da kuma Rivers.
An kashe mutane da dama da rikicin makiyaya a Benue da rikicin kabilanci a Taraba da kuma hare-haren barayi da 'Yan fashi a Zamfara.
Wannan dai na zuwa bayan shugaban ya sa suka a ziyarar da ya kai kano domin halartar auren 'yar gidan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Idris, dan gidan Gwamnan Oyo Abiola Ajimobi.
Shugaban ya fi shan suka a shafukan sada zumunta.
Masu amfani da shafukan sun soki shugaban na Najeriya da nuna rashin dattako kasancewar bai kai ziyara garin Dapchi ba, inda 'yan bindiga suka shiga makarantar Mata suka sace dalibai 110 a ranar 19 ga watan Fabrairu.
Haka kuma shugaban ya sha suka saboda rashin kai ziyara a jihohin da suka yi fama da kashe kashen mutane ba, kamar Benue inda aka kashe mutane sama da 70 a farkon watan Janairu.
Amma sanarwar ta ce, shugaba Buhari ya damu da abubuwan da suka faru, kuma a kullum yana tattaunawa da gwamnonin da abin ya shafa.
Shugaban ya yi kira ga 'yan Najeriya musamman wadanda ke yankunan da rikice-rikicen suka shafa su ba jami'an tsaro hadin kai domin kawo karshen matsalolin.
Source :bbc hausa
Title :
Buhari Zai kai Ziyara Benue, Dapchi, Da Zamfara
Description : Makwanni biyu bayan sace 'yan matan makarantar Dapchi 110 a jihar Yobe, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce zai kai ziyara a yankin...
Rating :
5