Kamfanin Sarrafa flawa na 'Flour Mills Nigeria Plc' ta bayyana cewa tana kusa kamalla shirye-shiryen kadammar da sashin sarrafa suga na kamfanin mai suna 'Sunti Golden Estate' da za'a bude a garin Mokwa na jihar Neja.
Masana'antar sugan da zai lashe maukuden kudi har naira biliyan 50 zai rika samar da sukari da adadin sa ya kai metric ton 100,000 a duk shekara.
Sanarwan da ta fito daga jami'an hulda da al'umma na kamfanin, Tola Samuel, ya ce ana sa ran shugaba Muhammadu Buhari ne zai kaddamar da masana'antar a ranar Alhamis, 15 ga watan Maris kamar yadda NAN ta ruwaito.
Sanarwan kuma ta ce gona sukari mai fadin hecta 17,000 da za rika samar wa masana'antar da rake zai samar ga ayyukan yi ga manoma 10,000 a duk shekara kuma kimamanin mutane 50,000 za su amfana ciki har da kananan manoma 3,000.
Ana sa ran masana'antar za ta rage adadin sugar da Najeriya ke siyowa daga kasashen waje kuma ta habbata tattalin arziki da rage talauci ta hanyar samar wa yan Najeriya ayyukan yi.
Source :naij hausa
Title :
Buhari Zai Gina Kamfanin Suga A Naija
Description : Kamfanin Sarrafa flawa na 'Flour Mills Nigeria Plc' ta bayyana cewa tana kusa kamalla shirye-shiryen kadammar da sashin sarrafa suga...
Rating :
5