Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Asabar din da ta gabata ya danganta shugabancin jam'iyyar adawa ta PDP da nutsewa cikin rudu da kuma kidahumanci na neman bambaron kitse siyasar su a zaben kasa mai gabatowa na 2019.
Rahotanni da sanadin jaridar Daily Trust sun bayyana cewa, jam'iyyar adawa ta PDP ta yi karar jam'iyyar APC da kuma hukumar zabe ta kasa zuwa ga majalisar dinkin duniya a bisa zargin su da shirya magudin zabe a 2019.
Shugaba Buhari da sanadin babban hadimin sa na musamman, Mallam Garba Shehu ya bayyana cewa, wannan lamari bai takaita ga abin dariya kadai ba domin kuwa ya haskaka irin damuwa da kuma yunwar kujerar mulki ta kowane hali da jam'iyyar PDP ke yi.
Mallam Garba yake cewa, sanya majalisar dinkin duniya cikin wannan lamari wata farfaganda ce kurum ta siyasa da ta bayyana karara irin shayin da jam'iyyar PDP ta ke yi na fuskantar masu jefa kuri'u a zaben 2019.
Ya ci gaba da cewa, ba bu abinda shugaba Buhari ya sanya a gaba a kasar nan face gudanar da zabe na adalci da ya tsarkaka da magudi domin kuwa tarihi ya tabbatar da hakan a zabukan jihohin Edo, Ondo da kuma Anambra.
Hadimin ya kara da cewa, a madadin jam'iyyar PDP ta ci gaba da nuna hali na farar Kura, ya kamata ta sake zage dantsen ta wajen kwakwulo yarda da amincin al'ummar kasar nan.
Source :naij hausa
Title :
Buhari Yayi Facali Da Jam'iyyar PDP
Description : Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Asabar din da ta gabata ya danganta shugabancin jam'iyyar adawa ta PDP da nutsewa cikin rudu da k...
Rating :
5