Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya bayyana sakin yan matan Dapchi da yan Boko Haram suka sace a jihar Yobe a matsayin nagartaccen shugabanci a karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
A wani jawabi da yayi ga manema labarai a Owerri tab akin babban sakatarensa, Mista Onwuemeodo, Okorocha yace wannan dalili shine abunda zai sa yan Najeriya su marawa Buhari baya.Jawabin ya zo kamar haka: “Da dawowar yan matan makarantar Dapchi 104 bayan an shafe kwanaki 30 da sace su, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna siyasa mai karfi saboda yadda ya dauki lamarin a matsayinsa na shugaban kasa wanda hakan ya nuna karfin shugabancin sa.
"Ya ci gaba da cewa: “Dawo da yan matan da akayi cikin gaggawa ya nuna jajircewar shugabancinsa saboda ba don jajircewar nasa ba toh da labara ya sha bambam a yanzu.
”A halin da ake ciki, al’umman garin Dapchi na jihar Yobe sun jaddada cewa bazasu taba rabuwa da tabon sace yayansu da yan ta’addan Boko Haram sukayi ba idan ba wai an dawo da Leah Sharubu bane.
Source :naij hausa
Title :
Buhari Ya Nuna Min Shi Nagartaccen Adali Ne -Rochas
Description : Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya bayyana sakin yan matan Dapchi da yan Boko Haram suka sace a jihar Yobe a matsayin nagartaccen shugaba...
Rating :
5