A yayin da ake murnar dawowar yan matan Dapchi guda 104 da mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram ta sako a ranar Laraba 21 ga watan Maris, su kuwa iyayen yan matan Chibok kokawa suka yi.Guda cikin Iyayen yan matan Chibok, Ayuba Alamson ya bayyana cewa gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari bata da wani kwakkwaran shirin kwato musu yayansu daga hannun Boko Haram.
Ayuba ya bayyana haka ne cikin wani hira da yayi da gidan rediyon BBC Hausa, inda yace inda gwamnati zata iya yin dalilin sako yan matan Dapchi cikin wata guda, kamata yayi ta yi sanadin sako yan matan Chibok da suka rage cikin kwana biyu.
Majiyar jaridar naij ta ruwaito shi yana cewa: “Mun gode ma Allah da ya dawo da yan matan Dapchi, kuma mun gode ma gwamnati da ma sauran mutanen Najeriya, amma mu iyayen yan matan Chibok muna kira ga gwmanati ta sake shiri don ganin an ceto mana yayanmu, don kuwa a yanzu bamu ga wani kwakkwaran shiri daga bangarenta ba.
”Ayuba yace a baya sun yi iya kokarinsu don ganin an ceto musu yayansu, inda yace har bin sawun yan ta’addan sun yi zuwa wani daji, inda suka iske su suna barci sun ajiye makamansu, amma gwamnati taki jajircewa don ceto yan matan.
A ranar 19 ga watan Feburairu ne dai yan ta’addan Boko Haram suka kunna kai cikin makarantar kimiyya dake garin Dapchi, inda suka yi awon gaba da dalibar 110, amma bayan kimanin wata guda suka dawo dasu sakamakon tattaunawa da gwamnati da suka yi.
Source :naij hausa
Title :
Buhari Ya Manta Da Ya Yanmu - Iyayen Matan Chibok
Description : A yayin da ake murnar dawowar yan matan Dapchi guda 104 da mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram ta sako a ranar Laraba 21 ga watan Mari...
Rating :
5