Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabuwar shirin tallafawa manoma da tarakta domin saukaka aikin noma domin cigaban da farfado da tattalin arzikin kasa.
Shugaban kasan ya kaddamar da wannan shiri ne a yau Juma’a, 9 ga watan Maris, 2018 a garin Jos, babban birnin jihar Plateau.
Jaridar NAIJ.com ta kawo muku cewa Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya isa filin jirgin saman Yakubu Gowon da ke garin Heipang jihar Flato misalin karfe 11:50 na safiyar Alhamis, 8 ga watan Maris, 2018.
Gwamnan jihar, Simon Lalong, tare da tsaffin gwamnonin jihar 2 kuma sanatoci a yanzu, Joshua Dariye da Jonah Jang; ministan wasanni, Solomon Dalung, tsohuwar mataimakiyar gwamnan jihar, Pauline Tallen da sauran su ne suka tarbesa a filin jirgin sama.
Ana sa ran shugaba Buhari zai kaddamar da wasu hanyoyi da gwamnan ya gina irinsu Mararaban Jama'a- Secretariat junction-British America junction road, Miango-Wild Life Park-Rafiki junction, Domkat Bali/Tudun Wada/old airport roundabout township roads da sauransu.
Source :naij hausa
Title :
Buhari Ya Bada Tallafin Kayan Gona A Filato
Description : Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabuwar shirin tallafawa manoma da tarakta domin saukaka aikin noma domin cigaban da farfado da tatt...
Rating :
5