Wani cikin kusoshin jam'iyyar PDP daga jihar Oyo, Wole Oyelese, ya nuna rashin jin dadinsa game da yanda ‘yan jam’iyyar ta su suka far masa a kan ra’ayinsa na tabbatar da cewa shugaba kasa Muhammadu Buhari baya aikata rashawa.
Kuma ya bayyana cewa ‘yan siyasa tun farko sun dauki siyasa a matsayin wata hanya ce ta yin kudi cikin sauri, ba wai don sun san menene siyasar ba.
Oyelese yace, “Ina maimaitawa cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari shine kadai mutumin da nake girmamawa, kuma ina nan kan bakana na cewa baya aikata rashawa”.
Oyelese ya kara da cewa, “Ina kalubalantar duk wanda keda shaidar wata takarda ta baki game da wasu makudan kudan kudi ko na sayen wani gini a Najeriya koma a fadin duniya wanda akace na Buhari ne wanda zai nuna cewa ya aikata rashawa, da ya kawo shaidako kuma yayi shuru da bakinsa.
”A wani cigaba, NAIJ.com tun kwanaki ta ruwaito cewa, tsohon shugaban kasa Shehu Shagari ya bukaci mutanen Najeriya da na kasashen waje da su goyi bayan Shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnatinsa, yace, yanada gaskia, baya aikata rashawa kuma shugaba ne da baya kabilanci.
Ya kara da cewa Buhari na yakar cin hanci da rashawa saboda haka yana bukatar addu’a da goyon bayan mutanen Najeriya.
Source :naij hausa
Title :
Buhari Mutum Ne Nagari - Jigon Jam'iyyar PDP
Description : Wani cikin kusoshin jam'iyyar PDP daga jihar Oyo, Wole Oyelese, ya nuna rashin jin dadinsa game da yanda ‘yan jam’iyyar ta su suka far m...
Rating :
5