Batun cewa Najeriya za ta taimakawa Ghana yakar cin hanci da rashawa a jawabin shugaba Buhari ya janyo cece-kuce a shafukan sadarwa na Intanet.
A ranar Talata ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ziyarci bikin cika shekara 61 da samun 'yancin kasar Ghana.
Kuma a wajen bikin, shugaban na Najeriya ya gabatar da jawabi, inda a ciki aka ruwaito ya ce zai taimakawa kasar Ghana yaki da rashawa.
Hakan ya sa wasu 'Yan Najeriya suka shiga shafukan sada zumunta a intanet suna sukar shugaban ta hanyar kalamai da hotunan ban dariya.
An yi wa jawabin da shugaba Buhari ya gabatar a Ghana fassara ne ta daban a kafofin yada labarai na talabijin da kuma na sadarwa a intanet.
A jawabinsa, Buhari bai ce zai taimakawa Ghana yakar rashawa ba, illa ya ce "Najeriya a shirye take ga duk wani shiri na hadin guiwa domin magance matsalar"
" Zan iya tabbatar wa da mai girma shugaban kasa cewa kana da abokin tafiya kamar yadda na ke sa ido ga duk wani nau'i na hadin kai tsakanin Najeriya da Ghana a kan yaki da rashawa".
Source :bbc hausa
Title :
Buhari Baice Zai Taimaka Wa Ghana Ba
Description : Batun cewa Najeriya za ta taimakawa Ghana yakar cin hanci da rashawa a jawabin shugaba Buhari ya janyo cece-kuce a shafukan sadarwa na Intan...
Rating :
5