Rahama Sadau tayi amfani da shafin sa na Tuwita ta bayyana cewa ba tayi hira da jaridar naij ba bayan da aka buga labari game da ita inda tace ba yau aka saba yi mata sharri.
Labari ya zo mana cewa fitaccen ‘Yar wasan kwaikwayon Najeriya Rahma Sadau ta musanta cewa tayi karin haske game da lokacin da za tayi aure.
‘Yar wasan fim din ta musanya cewa tayi hira da jaridar naij game da masoyan ta da kuma lokacin da za ta tare a gidan mijin ta. Dama a lokacin ta musanya cewa tana soyayya da babban Jarumin ‘Dan wasan Najeriya Ali Nuhu.
Rahma Sadau ta bayyana mana cewa kusan sau uku kenan ana buga labarai a kan ta wanda duk ba ta fadi hakan da bakin ta ba. Babbar ‘Yar wasan ta Nollywood tace ana kirkikar labarai ne da gan-gan a kan ta cikin ‘Yan kwanakin nan.
A rahoton baya kun ji cewa Jarumar Hausar ta bayyana cewa dukkan mace za ta so ta auri namiji irin Ali Nuhu musamman ma saboda mutum ne nagari, mai tausayi da kyautatawa wanda kuma su ne siffofin da duk wata mace ke nema.
Source :naij hausa
Title :
Bance Ga Wanda Zan Aura Ba, Sharri Akamin - Rahma Sadau
Description : Rahama Sadau tayi amfani da shafin sa na Tuwita ta bayyana cewa ba tayi hira da jaridar naij ba bayan da aka buga labari game da ita inda ta...
Rating :
5