Ma'aikatar aikin Hajji da Umara ta fitar da wata sanarwa, inda ta ce ayi watsi da wata jita-jita da ake wallafawa a shafukan sada zumunta kan cewa gwamnati za ta sanya wasu kudade na daban ga masu aikin hajji da umara da suka shigo daga kasashen ketare.
Jaridar Almadina da ake wallafawa da harshen larabci ita ta fara wallafa labarin a jiya litinin.
Inda ta yanko wani bangaren jita-jitar da aka wallafa ashafukan sada zumunta, kan cewa gwamnati za ta karbi Riyal 400 zuwa 700 ga duk wanda ya shigo kasar dan yin ibada da shekarunsa suka wuce 18.
Kuma wai ma'aikatar aikin hajji da umarar za ta kafa wasu cibiyoyi a filayen jiragen kasar da cikin birnin Makka dan karbar kudaden a hannu mutanen.
Gwamnatin ta tabbatar da babu wannan batun sam, amma ta na shirin sake fadada girman wuraren da Alhazai za su zauna wanda a halin da ake ciki wuraren sun yi kadan saboda an yi su ne dan mutane miliyan Takwas zuwa miliyan Goma sha Biyar kamar yadda tsarin shekarar 2020 ya tanada.
Amma yanzu za a fadada shi zuwa na mutane miliyan 30, ana kuma sa ran za a yi aikin ne daga yanzu zuwa shekarar 2030.
Source :bbc hausa
Title :
Bamu Kara Wa Mahajjata Haraji Ba-Saudiyya
Description : Ma'aikatar aikin Hajji da Umara ta fitar da wata sanarwa, inda ta ce ayi watsi da wata jita-jita da ake wallafawa a shafukan sada zumunt...
Rating :
5