Gwamnatin jihar Legas ta ce dokar hana makiyaya yawo da dabobin a cikin jihar yana nan kuma zata gurfanar da duk wanda ta kama ya saba dokar.
Kwamishinan harkar noma na jihar Legas, Oluwatoyin Suarau, ya bayyana haka a karshen makon da ta gabata a lokacin da yake bibiyar sakamakon rahoto akan dobobin dake yawo jihar ba tare da kulawar ma su shi ba, da kuma masu sufurin dabobi a jihar.
Sarau ya ce jihar Legas baza ta cigaba da amincewa da irin balao’in da dabobin dake yawo akan manyan titunan jihar ke jawo wa ba, kuma jihar Legas ashirye take ta hana yawo da dabobi a cikin jihar
.Yawo dabbobin da basu da lasisi za su iya janyo hatsari da cututuka kamar, tarin fuka, Cizon kare da sauran su.
Sarau yayi ikrarin cewa gwamnatin jihar Legas na yanzu zata ginawa dabobi hanya na musamman da za a rika bi da su a cikin garin kamar yadda ake da su a kasashen da suka cigaba.
Source :naij hausa
Title :
Bamu Amince Wani Makiyayi Ya Shigo Da Dabbobin Sa Cikin Gari Ba-Gwamnatin Legas
Description : Gwamnatin jihar Legas ta ce dokar hana makiyaya yawo da dabobin a cikin jihar yana nan kuma zata gurfanar da duk wanda ta kama ya saba dokar...
Rating :
5