Yan majalisar jam'iyyun hamayyar Ghana sun ki amincewa da yarjejeniyar da kasar ta kulla domin Amurka ta aika da dakaru da kayan yaki kasar.
A zaman da majalisar ta yi ranar Juma'a, ta amince da bukatar bangaren zartawa domin a bar Amurka ta aika da dakarun kasar, yayin da ita kuma za ta ba da $20m sannan sojinta su samu horo.
Sai dai 'yan majalisar jam'iyyun hamayyar sun yi fatali da bukatar inda suka fice daga zauren majalisar domin nuna rashin amincewarsu.
Sun kara da cewa yarjejeniyar za ta cutar da kasar da kuma sarayar da 'yancinta na kasancewa kasa mai cin gashin kanta.
Amurka dai tana so ta ci gaba da kai dakarunta yammacin Afirka a yayin da mayakan da ke ikirarin jihadi ke mamaye yankin.
Source :bbc hausa
Title :
Bamu Amince A Turo Mana Dakarun Amurka Ba - Majalisar Ghana
Description : Yan majalisar jam'iyyun hamayyar Ghana sun ki amincewa da yarjejeniyar da kasar ta kulla domin Amurka ta aika da dakaru da kayan yaki ka...
Rating :
5