Jami’ai sun bayyana cewa wani dan kunar bakin wake ya tayar da Bam a babban birnin kasar Afghanistan, Kabul, a yau Juma’a, inda akalla mutane 7 suka hallaka.
Dan kunar bakin waken ya kai wannan hari ne domin kasha mabiya akidar Shi’a dake taro a yau.
Mataimakin ministan harkokin cikin gidan kasar, Nasrat Rahimi, ya ce dan sanda daya da masu farar hula 6 ne suka rasa rayukansu yayinda wasu 6 suka jikkata.
Ya ce dan kunar bakin waken ay nufi taron yan Shi’a inda suka murnan kisan Abdul Ali Mazari,wanda Taliban suka kasha a shekaran 1995.
Kafin yanzu, an dade ana kai hari masallatan Shi’a kuma kungiyar ISIS na daukan alhakin wadannan hare-hare duk da cewa jami’a tsaro na shakkan cewa su kadai ke yi.
A watannin Oktoba zuwa Disamban da ya gabata, an kashe akalla mutane 72 a kunar bakin wajen a tarukan mabiya akidar Shi’a.
Source :naij hausa
Title :
Bam Yatashi Agun Taron 'Yan Shi' a
Description : Jami’ai sun bayyana cewa wani dan kunar bakin wake ya tayar da Bam a babban birnin kasar Afghanistan, Kabul, a yau Juma’a, inda akalla mutan...
Rating :
5