Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust cewa wasu Inyamuran kasar nan sun bayyana tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso a matsayin ‘Dan takarar su na Shugaban kasar Najeriya a zabe na gaba.
Wata Kungiyar siyasa ta Tarayyar Inyamurai ta AIPPG ta bakin Shugaban ta Lady Rosemary Ukiwe ta bayyana cewa babu wanda ya cancanci ya rike Najeriya irin tsohon Gwamna kuma Sanatan Jihar Kano na yanzu.
Kungiyar kamar yadda Sakataren ta watau Romanus Azubuike ya bayyana duk Arewacin kasar ba su samu wanda ya dace ya rike Najeriya ba irin Kwankwaso saboda irin namijin kokarin da yayi lokacin yana Gwamnan Kano.
Inyamuran sun nuna cewa tafiyar Kwankwasiyya ita ce ta hada yara da kuma manya don haka su ke ganin ya kamata a ba Kwankwaso wanda mutum ne mai jini-a-jika da kuma shekaru dama ya jarraba sa’ar sa a matsayin Shugaban kasa.
Source :naij hausa
Title :
Babu Wanda Zai Iya Gyara Nijeriya Sai Kwankwaso - Inyamurai
Description : Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust cewa wasu Inyamuran kasar nan sun bayyana tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso a matsayi...
Rating :
5