Sanata mai wakiltar jihar Kogi ta yamma, Dino Melaye, ya musanta rahoton jaridar Sahara Reporters cewar ya gudu daga Najeriya da niyyar ba zai dawo ba sai an samu canjin gwamnati a matakin jiha da kuma na tarayya.
Jaridar Sahara Reporters ce ta fara rawaito cewar Sanata Melaye baya Najeriya a yanzu haka, kuma ya gudu ne bayan hukumar ‘yan sanda ta kama wasu ‘yan ta’adda a jihar Kogi da suka ce Sanatan ne ke basu kudi da makamai domin tayar da hankulan jama’a a jihar.
Saidai, Sanatan ya ce jaridar ta sharara, karya kawai ta sharara a kansa kamar yadda ta saba tare da bayyanawa jaridar Premium Times cewar ya fita waje ne domin gudanar da wasu aiyuka, aiyukan da bai bayyanawa jaridar ko wadanne iri bane, sannan bai fadi ranar dawowar sa Najeriya ba.
Jaridar Sahara ta rawaito cewar, kafin fitar sa daga Najeriya, Sanata Melaye, ya bukaci shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, da wasu ‘yan majalisar ta dattijai das u tabbatar sun kare shi ko kuma ya tona asirin dai kai ga Sanatoci fiye 30 asarar kujerar su.A martininsa da ya fitar kuma ya aikewa jaridar Premium Times, Melaye, y ace babu yadda za ai ya gudu ya bar Najeriya, ya bar iyalinsa da abokan arziki yayin da babu dalili ko bukatar yin hakan.
Melaye na fuskan tuhuma daga hukumar ‘yan sanda bayan fuskantar barazanar kiranye daga mazabar sa, matsalolin day a zargi gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, da hukumar ‘yan sanda da kitsa su.
Source :naij hausa
Title :
Ba Guduwa Nayi Daga Nijeriya Ba - Dino Melaye
Description : Sanata mai wakiltar jihar Kogi ta yamma, Dino Melaye, ya musanta rahoton jaridar Sahara Reporters cewar ya gudu daga Najeriya da niyyar ba z...
Rating :
5