Kwamishinan raya birni da karkara na Jihar Kano, Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso, ya ce dan majalisar mai wakiltar Kano ta tsakiya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, kila ya jawowa kansa kora da ga jam’iyar ta APC, sakamakon watsi da ya yi da kiran da kungiyar tayi ma shi wadda Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yake jagoranta.Iliyasu Kwankwaso ya ce jam’iyar za ta zama ba tsari idan har ba a hukunta Dan Majalisar ba, musamman na kin amsa kiran Shugaba Muhammadu Buhari da wasu manyan jam’iya.
Kwamishinan wanda dan uwa ne ga Dan Majalisar, ya fadawa manema labarai a jiya cewa, kungiyar karkashin jagorancin Bola Tinubu ta gayyaci Kwankwaso zuwa bikin 'yar Gwamnan jihar Ganduje don sasanta tsakanin su, amma dan majalisar ya zabi yin watsin da gayyar wanda hakan ke nuna bai shirya sasantawar ba.
Kwamishinan ya kara da cewa wannan rashin daraja kiran da akayi ma sa da kuma halayyar da ya ke nunawa na nufin ya bar jam’iyar mu ta APC, da ma tuni ya zabi ya bi ‘yan Kungiyar Obasanjo.
An gayyace shi bikin ne musamman dan a daidaita tsakanin sa da Gwamnan amma yaki zuwa, wanda hakan ya sa ina mai tabbatar muku da cewar ya na hanyar barin ‘jam’iyar.Iliyasu Kwankwaso ya ce ko Sanatan da abokan tafiyar sa na so ko basa so Ganduje da Buhari ba wai takara kadai zasu tsaya ba, sai sun ci zaben 2019.
Ya ce, ba wai ra’ayin Buhari na tsayawa takara ko kin tsayawa ba, magana ce ta abun da jam’iya da mutanen Najeriya suka riga suka yanke hukunci a kai tuntuni, saboda sun riga sun bashi hadin kai da goyon baya.
Source :naij hausa
Title :
APC Zata Iya Korar Kwankwaso Daga Jam'iyyar
Description : Kwamishinan raya birni da karkara na Jihar Kano, Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso, ya ce dan majalisar mai wakiltar Kano ta tsakiya, Sanata Rab...
Rating :
5