Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma babban dan siyasa Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa jam'iyyar APC ta basu kunya musamman ma ganin yadda suna yabon ta sallah amma sai gashi ta kasa alwalla.
Atiku din ya yi wannan ikirarin ne a lokacin da ya jagoranci wasu jiga-jigan jam'iyyar ta sa ya zuwa gidan gwamnatin jihar Ribas a jiya inda aka ruwaito ya ayyana kudurin yin takarar shugaban kasa a 2019.
Jaridar NAIJ ta samu haka zalika cewa shahararren dan siyasar ya kuma yi kira ga 'yan Najeriya da su tabbatar da ganin sun fatattaki jam'iyyar ta APC daga madafun iko a zaben mai zuwa musamman saboda alkawurran da suka kasa cika masu.
Source :naij hausa
Title :
APC Ta Gagara Tabuka Komai Wa Nijeriya - Atiku
Description : Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma babban dan siyasa Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa jam'iyyar APC ta basu kunya musam...
Rating :
5