Miliyoyin mata a Spaniya sun shiga yajin aiki wanda irinsa ne na farko a kasar. Sun yi wa zanga-zangar lakabi da "Idan muka tsaya, duniya ma za ta tsaya".
Yajin aikin dai na nuna kin amincewa da rashin daidaito tsakanin jinsi ne da kuma cin zarafin mata.
Kungiyoyin kasuwanci sun mara wa masu shirya yajin aikin baya, inda hakan ya sa Spaniya ta yi fice daga sauran kasashen duniya dari da saba'in da su ka yi bikin ranar mata ta duniya.
Sama da zanga-zanga dari uku a ka shirya da maraice, kuma masu shiryawar sun ce sun samu goyon baya fiye da yadda suke zato.
Wani bincike ya nuna cewa sama da kashi tamanin cikin dari na 'yan Spania na goyon bayan daidaito tsakanin jinsi.
Source :bbc hausa
Title :
Anyi Zanga Zangar Mata Zalla A Spaniya
Description : Miliyoyin mata a Spaniya sun shiga yajin aiki wanda irinsa ne na farko a kasar. Sun yi wa zanga-zangar lakabi da "Idan muka tsaya, duni...
Rating :
5