Babban Kotun Tarayya da ke zama a Birnin Tarayya Abuja yayi watsi da karar da aka kawo gaban sa da yunkurin cire Gwamnan Jihar Kogi Alhaji Yahaya Bello daga ofis a makon nan. Bello ya samu hawa mulki ne bayan rasuwar Abubakar Audu.
Alkali mai shari’a John Tsoho a Ranar Talata yayi facali da karar da ake yi na sauke Gwamna Yahaya Bello daga kujerar Gwamna. Alkali Tsoho yace Lauyoyin da su ka shigar da kara ba su da ta cewa a kan maganar kujerar Gwamnan.
Manyan Lauyoyin kasar nan Michael Elokun, Ibrahim Sule da kuma Hauwa Audi sun nemi Kotu ta tsige Yahaya Bello tayi maza ta maida tsohon Gwamna Idris Wada kan kujerar sa.
Kotu dai ba ta ga dalilin yin wannan ba a zaman da tayi a Ranar Talatan nan.
Alkalin yace wadanda su ka shigar da karar ba ‘Ya ‘yan APC mai mulki bane kuma ba su yi takara a zaben na Gwamnan Jihar Kogi ba don haka babu dalilin zuwa Kotu. Asali ma dai Alkalin yace wannan matsala ce ta fitar da gwani Jam'iyya ba zabe ba.
Source :naij hausa
Title :
Anyi Yunkurin Cire Gwamnan Kobi
Description : Babban Kotun Tarayya da ke zama a Birnin Tarayya Abuja yayi watsi da karar da aka kawo gaban sa da yunkurin cire Gwamnan Jihar Kogi Alhaji Y...
Rating :
5