A ranar Larabar da ta gabata ne, fitaccen attijirin nan na duniya Bill Gates tare da Alhaji Aliko Dangote, suka rattaba hannu kan wata yarjejeni da gwamnoni shidda na yankin Arewa domin inganta harkokin alluran riga-kafi.Gwamnonin sun hadar da; Aminu
Waziri Tambuwal na jihar Sakkwato, Kashim Shettima na jihar Borno, Abdullahi Ganduje na jihar Kano, Muhammad Abubakar na Bauchi da kuma Nasir El-Rufa'i na jihar Kaduna.
Jaridar naij ta ruwaito cewa, gwamnan jihar Yobe Ibrahim Gaidam, bai halarci wannan taro ba yayin da Dakta Bello Kawu ya wakilce shi a birnin na Shehu.
Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito cewa ministan lafiya, Farfesa Isaac Adewole ya shaidi wannan taro da aka gudanar tare da halartar sarakunan gargajiya.
A na sa jawabin, Bill Gates ya bayyana cewa wannan jarjejeniya za ta yi hobbasa tare da taka muhimmiyar rawa wajen wadatuwar allurorin riga-kafi da kuma magunguna ga kananan yara.
Jaridar naij ta fahimci, gawurtaccen attajirin dai ya hallara a kasar Najeriya tun a makon da ya gabata, inda ya halarci bikin diyar Dangote na gani na fade da aka gudanar.
Source :naij hausa
Title :
Anyi Yarjejeniya Tsakanin Dangote, Bill gate Da Gwamnonin Arewa Guda 6
Description : A ranar Larabar da ta gabata ne, fitaccen attijirin nan na duniya Bill Gates tare da Alhaji Aliko Dangote, suka rattaba hannu kan wata yarje...
Rating :
5