Wasu 'yan bindiga sun da ba a tantance ba sun sace matar wakilin kafar yada labarai ta VOA da kuma Dansa a Kaduna da ke arewacin Najeriya.
Maharan kuma sun kashe wani jami'in hukumar kiyaye hadurra ta FRSC da suke makwabtaka da wakilin na VOA Nasir Birnin Yaro.
Birnin Yaro ya tabbatarwa da wakilin BBC Nura Muhammad Ringim da faruwar al'amarin, inda ya ce maharan sun shiga ne a tsakiyar dare.
Ya ce lokacin da suka shiga gidansa da ke Birnin Yaro, ba ya nan amma sun iske iyalinsa suna tambayar matarsa inda yake.
A lokacin ne kuma suka harbe makwabcinsa Sabitu Abdulhamid jami'in hukumar kiyaye hadurra FRSC bayan ya shiga gidan da nufin taimakawa iyalinsa.
Kuma ayan sun kashe shi ne suka tafi da matarsa da dansa.
Birnin Yaro ya ce yana tunanin sun shigo gidansa ne da nufin su yi garkuwa da shi, amma da ba su same shi ba suka tafi da iyalinsa.
Kaduna dai na cikin yankunan arewacin Najeriya da ke fama da matsalar sace-sacen mutane kuma matsala ce da ta ki ci ta ki cinyewa.
Source :bbc hausa
Title :
Anyi Awun Gaba Da Matar Wakilin VOA Da Dansa A Kaduna
Description : Wasu 'yan bindiga sun da ba a tantance ba sun sace matar wakilin kafar yada labarai ta VOA da kuma Dansa a Kaduna da ke arewacin Najeriy...
Rating :
5