Labaran da muke samu daga majiyoyin mu na nuni da cewa akalla mutane uku (3) ne suka jigata tare jin raunuka kala-kala bayan da magoya bayan jam'iyyar APC mai mulki a tarayya da kuma jam'iyyar adawa ta PDP dake mulki a jihar Bayelsa dake a kudu maso kudancin Najeriya.
Mun samu dai cewa wannan artabun ya faru ne a karamar hukumar Brass a jihar yayin da magoya bayan dan majalisar jihar na jam'iyyar APC mai suna Israel Sunny-Igoli da kuma magoya bayan shugaban rikon kwaryar kwamitin karamar hukumar mai suna Mista Victo Isaiah.
Jaridar naij dai haka zalika ta samu cewa fadan ya kazanta sosai yayin da dukkan bangarorin biyu suka fitar da munanan makamai suka farwa junan su irin su bindugun gargajiya da kayan aikin gona.
A wani labarin dai, mun samu cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta gwamnatin tarayyar Najeriya watau Independent National Electoral Commission, INEC a takaice ta sanar da wasu muhimman sauye-sauye a kan yadda za ta gabatar da zaben shekarar 2019 mai zuwa.
Mun samu cewa hukumar ta zaben ta Independent National Electoral Commission, INEC ta ta bakin kwamishinan ta na jihar Imo Farfesa Francis Ezeonu ya bayyana cewa ba za su yi anfani da fom din nan ba na rubuta kura-kuran da aka samu watau Incident Form.
Source :naij hausa
Title :
Anyi Artabu Tsakanin Magoya Bayan Jam'iyyar APC Dana PDP A Bayelsa
Description : Labaran da muke samu daga majiyoyin mu na nuni da cewa akalla mutane uku (3) ne suka jigata tare jin raunuka kala-kala bayan da magoya bayan...
Rating :
5