Sifeto Janar na hukumar yan sanda, Ibrahim Idris, ya bada umurnin sallamar kwamishanan yan sandan jihar Kogi, Ali Janga, a yau Laraba 28 ga watan Maris, 2018.
An sallami Ali Janga ne tare wasu manyan hafsoshin yan sana da ke aiki karkashinsa kan rawan da suka taka wajen tserewan wasu yan bindigan da ke yiwa sanata Dino Melaye aiki daga kurkukun yan sanda a jihar.
Yan bindigan wadanda suka bayyana cewa Sanata Dino Melaye ne mai daukan nauyins ta hanyar basu kudi da makamai sun tsere da safyar yau Laraba, gab da su bayyana a gaban babban kotun tarayya da ke Lokoja, babban birnin jihar Kogi.
Sifeton yan sandan ya umurci CP Esa Sunday Ogbu, kwamishanan ayyukan tarayya na shelkwatan yan sanda ya maye gurbinsa da wuri.
Source :naij hausa
Title :
Ankori Kwamishinan Yan Sanda Na Jihar Kogi
Description : Sifeto Janar na hukumar yan sanda, Ibrahim Idris, ya bada umurnin sallamar kwamishanan yan sandan jihar Kogi, Ali Janga, a yau Laraba 28 ga ...
Rating :
5