Jami’an yan sandan RSS sun kama wani mahaukacin karya a karkashin gadar Eko bridge dake jihar Lagas.
Mutumin wanda ya bayyana kansa a matsayin Oyahere Johnson, mai shekaru 35 daga Port Harcourt ya tona asirin cewa yana amfani da bindigar wasan ne wajen yiwa mutane fashi.
Ya bayyana cewa yana amfani dab akin bindigan wasa wanda yayi kama da bindigar Baretta wajen yiwa masu wucewa fashin kudade da sauran kayayyaki.
Jami’an yan sanda RRS ne suka kama shi bayan wani dan achaba ya kai masu rahoto da misalign karfe 11 na dare a ranar Lahadi, 4 ga watan Maris.
Jami’an sun je wajen da abun ke afkuwa cikin gaggawa sannan kuma suka gano mutumin inda ya boye bindigar a wandonsa sannan yayi yunkurin guduwa.
Source :naij hausa
Title :
Ankama Wani Mahaukacin Karya Da Bindiga A Legas
Description : Jami’an yan sandan RSS sun kama wani mahaukacin karya a karkashin gadar Eko bridge dake jihar Lagas. Mutumin wanda ya bayyana kansa a matsa...
Rating :
5