Hukumar kwastom a Najeriya ta kama wani dan kasar China da mai gadinsa da hauren giwa sama da dari biyu da kuma sassan wata dabba mai daraja da ake kira Pangolin har buhu hamsin da biyar.
Hukumar ta kama mutanen ne a Ikeja, jihar Legas bayan wasu bayanan sirri da suka samu cewa akwai hauren giwa mai yawa da watakila ake shirin ketarawa da shi kasashen waje.
Konturola na kwastom mai kula da shiyyar kudu maso yammacin Najeriya, Muhammad Uba Garba ya shaida wa BBC cewa hauren giwan na da daraja a kasuwar duniya da kuma sassan dabbar Pangolin wadda ake sassake bawon jikinta, ana rigunan saki na kasaita ga sarakuna da masu hali.
Tuni dai hukumar kwastom ta mika kayayyakin ga hukumar kula da gandun daji da muhalli ta Najeriya.
Yanzu haka za a fara bincike domin gano ko ana shirin ketarawa ne ko shigo da sassan dabbobin na giwa da kuma Pongolin.
An kama yawan hauren giwa har buhu 218 da kudinsu ya haura naira miliyan tamanin da biyar sai kuma dabbar ta Pangolin buhu hamsin da biyar da kudinsu ya haura naira miliyan dari hudu.
Ana fasakwaurin hauren giwa zuwa China
An dai haramta fasakwaurin sassan giwa kamar yadda konturola na kwastom, Muhammad Uba ya shaidawa BBC.
Kuma ya ce kasar China a yanzu ma tana nesanta kan ta daga fasakwaurin hauren giwar da rahotabin ke cewa can ake kai wa.
Shin hana kasuwancin hauren giwa a China zai kare giwaye?
Shugaban Kenya ya kona dubban hauren Giwa
Masana harkokin dabbobi sun nuna giwaye da kuma dabbar Pangolin mai daraja na fuskantar barazanar karewa a doron kasa. Hakan kuwa na farauwa a sakamakon yadda ake farautar dabbobin ba bisa ka'ida ba.
Ana dai amfani da hauren giwar da kuma sassan dabbar ta Pangolin domin abubuwan kawa.
Sannan ana amfani da sauran sassan jikin dabbar ta Pangolin don hada magunguna masu karfi, kuma mafi yawanci bil'adama na amfani da shi don kara kyawon jiki da karfi.
Sassan jikin Dabbar Pangolin
Wasu rahotanni dai na cewa ma su sana'ar sassan dabbobin giwa na neman mayar da Najeriya wani zangon shigowa da fita da hauren giwa da sassan jikin dabbar Pangolin zuwa kasashen turai ko kuma China ta barauniyar hanya.
A nan gaba ne dai ake shirin gurfanar da mutanen a gaban kotu.
Source :bbc hausa
Title :
Ankama Wani Bachanike Da Hauren Giwa Sama Da 200 a Legas
Description : Hukumar kwastom a Najeriya ta kama wani dan kasar China da mai gadinsa da hauren giwa sama da dari biyu da kuma sassan wata dabba mai daraja...
Rating :
5