Jami'an rundunar hana shige da fice ta kwastam shiyyar jihar Sokoto sun sanar da samun nasarar kama wata tankar dakon man fetur dauke da jarakunan man abinci akalla 446 sannan kuma yanzu haka suna cigaba da tsare direban tankar da dan rakiyar sa.
A cewar shugaban rundunar shiyyar, Mista Nasir Ahmed ya bayyana cewa sunan Bamus Global Co. Ltd ne kuma aka rubuta a jikin tankar kuma an kamata ta ne akan hanyar Sokoto zuwa Gusau yayin da jami'an sa suke sintiri.
Jaridar naij dai ta samu wannan nasarar da jami'an kwastam din suka samu na zuwa ne mako daya kacal bayan sun kama wata tankar makare da shinkafa mai guba a kan iyakar jihar Sokoto da Nijar din.
A wani labarin kuma, Gwamnatin jihar Sokoto karkashin jagorancin gwamnan jihar Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ta amince da fitar da zunzurutun kudi har Naira miliyan 7.9 domin biyan kudin magunguna da kuma na asibiti ga masu karamin karfi dake zaune a jihar.
Shugaban hukumar Zakka da wakafi na jihar ne dai Malam Lawal Maidoki ya sanar da hakan ga manema labarai lokacin da yake rarraba kudaden ga wasu asibitoci da dakunan shan maganin da jihar ta ware domin shirin.
Source :naij hausa
Title :
Ankama Tankar Mai Makare Da Kayan Abinci A Arewa
Description : Jami'an rundunar hana shige da fice ta kwastam shiyyar jihar Sokoto sun sanar da samun nasarar kama wata tankar dakon man fetur dauke da...
Rating :
5