Yan sanda sun kama wani mutum da yake karyar cewa shi Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ne a shafin Instagram.
Matashin mai shekara 20 yana da mabiya fiye da 200,000 a Instagram, har ma kuma ya samu damar da kamfanin Instagram ya tantance shi ta hanyar ba shi shudiyar alama.
Shafin dai ya kasance na sirri ne da sai an amince kafin ka fara bin sa duk da cewa yana da alamar tamntancewar.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Kano Musa Magaji Majiya ya shaida wa BBC cewa ana ci gaba da bincike, kuma za su tuhumi mutumin nan ba da jimawa ba da laifin yin sojan gona da kuma zamba.
Ya kara da cewa Sarkin na daga cikin mutum bakwai da aka yi sojan gona da sunansu, da suka hada da wasu manyan 'yan kasuwa da manyan masu fada a ji.
'Yan sanda sun ce mutumin da ake tuhumar ya samu mabiya a kalla miliyan uku a dukkan shafukan bogin da ya bude na kafafen sada zumunta.
Bai fadi dalilin da ya sa yake shigar sojan-gonar ba, amma bude shafuka mai dumbin mabiya irin haka na iya zama hanyar samun kudi ta hanyar samun tallace-tallace.
Kamfanino Instagram dai ya ce shafukan manyan mutane kawai yake sanyawa alamar shudi na tantancewa saboda gudun yi musu sojan-gona.
Shafin intanet din kamfanin ya ce: "Muna so mu tabbatar da cewa mutanen da ke amfani da Instagram za su iya saurin gane ko wadanda suke bi na gaskiya ne ba sojan-gona ba."
Babu inda Musulunci ya ce ka doki matarka — Sarki Sunusi
A shirye nake na yi gwajin miyagun kwayoyi — Sarki Sanusi
Gwamnatin Nigeria ta ki daukar mataki kan kisan Fulani 800 —Sarki Sanusi
A watan janairun 2018 ma rundunar 'yan sandan Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, sun ce sun kama wata mata da ke yin sojan-gona a matsayin mai dakin shugaban kasar Aisha Buhari.
Sanarwar ta kara da cewa jami'an 'yan sandan sun kama ta ne ranar 10 ga watan Janairu bayan sun samu rahotannin da ke cewa ta nemi taimakon kudi a wurin wani jami'in hukumar Fadama III Project.
Wane ne Sarkin Kano?
Sarki Muhammad Sanusi II shi ne tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN
An sauke shi daga mukamin a shekarar 2014 bayan da ya bankado wata badakalar batan dala miliyan 20 na man fetur
Mujallar The TIME ta sanya sunansa a jerin fitattun mutane na 2011
A shekarar 2013 aka ba shi wata muhimmiyar kyauta a wajen wani taron koli kan harkokin hada-hadar kudi na musulunci sabodagudunmowar da yake bayar wa ga bunkasar hada-hadar banki da kudade bisa tsari na msuulunci.
Shi ne Sarki na 14 a jerin sarakunan Fulani na Kano, kuma jika ne ga Sarkin Kano na 11, Sarki Muhammadu Sunusi I.
Source :bbc hausa
Title :
Yan Sanda Sunkama Sarkin Kano Na Bogi
Description : Yan sanda sun kama wani mutum da yake karyar cewa shi Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ne a shafin Instagram. Matashin mai shekara 20 yana d...
Rating :
5