Akalla mutane 6 sun ji raunuka iri-iri yayinda wasu yan baranda suka kaiwa Hausawa yan kasuwan canji da ke kasuwan Ekiosa da ke karamar hukumar Oredo, jihar Edo.An yi rikici a kasuwan yayinda yan barandan sukayi kokarin cutan hausawan amma Hausawan sukayi jan wuya, suka ki yarda.
Daya daga cikin yan Hausawan, Muhammadu Basiru, wanda yace an sace masa kuyi ya bayyana cewa daya daga cikin yan barandan mai suna Osazee ya kasance yana zuwa nan yana rokon kudi amma yau, ya gayyaci wasu abokansa domin suyi mana fashi.
Shugaban Hausawan jihar, Alhaji Badamasi Saliu, yayinda yake jawabi da manema labarai cewa yana ofishinsa sai aka kirasa cewa wasu yan daba sun kaiwa Hausawa hari a kasuwan Ekiosa.
Yace duk da cewan ba’a san yawan kudinda suka sata ba har yanzu, jami’an tsaro sun dakile rikicin a Kasuwan.
Mal Badamasi ya kara da cewa ba’ayi rashin rayuwa ba amma an samu munanan raunuka yayinda aka fara sa’insa.
Kakakin hukumar yan sandan jihar, DSP Chidi Nwanbuzor, wanda ya tabbatar da wannan labari ya ce hukumar ta dakile rikicin.
Source :naij hausa
Title :
Ankaiwa Hausawa Mazauna Edo Hari
Description : Akalla mutane 6 sun ji raunuka iri-iri yayinda wasu yan baranda suka kaiwa Hausawa yan kasuwan canji da ke kasuwan Ekiosa da ke karamar huku...
Rating :
5