Yanzu haka ana cikin zaman dar dar a tsakanin manyan shugabannin hukumar rundunar 'yan sandan Najeriya bayan da wani bincike na hukumar harkokin kudi ya bankado akalla jami'an 'yan sanda dubu 78 da dari 315 na bogi da kuma gwamnati ke biya albashi duk wata.
Haka zalika ma dai ma'aikatar kudin ta gwamnatin tarayyar ta kuma bayyana cewa ta samu nasarar yin tsime na akalla Naira biliyan 68 na kudaden gudanarwa a cikin shekarar ta 2017.
Wannan nasarar da aka samu dai kamar yadda muka samu daga majiyoyin mu na fadar shugaban kasar, ta samu ne biyo bayan wani yunkurin gwamnatin na yin gyara tare da mayar da harkokin albashin ma'aikatar a bisa tsari na bai daya da ake yiwa lakani da Integrated Payroll and Personnel Information System (IPPIS) a takaice.
A wani labarin kuma dai, 'Yan majalisar wakilan Najeriya a ranar Alhamis din da ta gabata sun saka alamar tambaya akan kwamitocin shugaban kasa ke fawa na binciken wasu badakalolin da ake zargin an tafka a gwamnatance inda suka bayyana su a matsayin masu shiga aikin wasu ma'aikatun gwamnati masu zaman kansu.
Tuni dai majalisar a karkashin jagorancin kakakin ta Yakubu Dogara ta amince da a gudanar da bincike kan lamarin da nufin lalubo hanya daya sahihiya da zata kawo karshen cin karo da junan da ake samu a dalilin hakan.
Source :naij hausa
Title :
Angano Yan Sandan Bogi 78, 315 A Kasarnan
Description : Yanzu haka ana cikin zaman dar dar a tsakanin manyan shugabannin hukumar rundunar 'yan sandan Najeriya bayan da wani bincike na hukumar ...
Rating :
5