Daily Trust tace an gano cewa dai akwai ma’ikatan bogi na kin-karawa a Najeriya wanda hakan ya sa Gwamnatin Shugaba Buhari ta adana kudi har sama da Naira Biliyan 200 cikin shekaru 2.
Gwamnatin Shugaba Buhari ta kawo wani tsari da yayi bincike domin gano ainihin ma’aikatan kasar shekaru biyu da su ka wuce. A wannan bincike an gano kudi sama da Naira Biliyan 208 da su ke tafiya a iska da sunan albashin mutanen da babu su a Duniya.
Dr. Mohammed K. Dikwa wanda shi ne Sakataren wannan kwamiti na PICA da Shugaban kasa ya nada yace an gano Ma’aikatan bogi 50, 000 da kuma Ma’aikata 300 da su ke karbar albashi bayan sun bar aiki. An kuma gano da dama da ke karbar albashi har biyu.
Gwamnatin Buhari ta kuma rage kudin da ake ba Ministoci da Ma’aikatu da kuma alawus din Hukumomin lafiya.
Bayan nan kuma kun ji cewa an yi binciken albashin da Jami’an tsaro ke karba inda aka gano tarin Ma’aikatan bogi shi ma a wannan bangaren.
Source :naij hausa
Title :
Angano Ma'aikatan Bogi Sama Da 50,000 A Kasarnan
Description : Daily Trust tace an gano cewa dai akwai ma’ikatan bogi na kin-karawa a Najeriya wanda hakan ya sa Gwamnatin Shugaba Buhari ta adana kudi har...
Rating :
5