Masu shigar da kara a Iran sun ce an yankewa wata mata hukunci daurin shekara biyu, saboda cire mayafinta da ta yi a bainar jama'a don nuna adawa da tsauraran dokokin sanya sutura na kasar.
An samu matar ce, wadda ba a bayyana sunanta ba a hukumance, da laifin "gurbata tarbiyyar al'umma", a cewar babban mai shigar da kara na Iran Abbas Jafari-Dolatabadi.
Sai dai ya ce an dakatar da hukuncin daurin nata, domin tana batu na rashin lafiya.
Wannan na zuwa bayan an kame wasu mata da dama a Iran a makwannin da suka gabata.
Amma an saki yawancin wadanda aka kame saboda sun saba dokokin kasar na rashin sanya hijabi a bainar jama'a.
Kuma an sake su ne ba tare da an caje su ba.
A ranar Laraba ne a birnin Tehran aka yanke wa matan hukuncin daurin watanni uku.
Amma tana matukar bukatar kula da lafiyarta, dalilin da ya tilasta aka ba likitar damar diba ta, a cewar Jafari-Dolatabadi.
Ya kalubalanci dakatar da hukuncin da aka yanke wa matar, yana mai cewa dole sai ta yi kwanakin da aka yanke ma ta a gidan yari.
A watan Disemba, irin wannan ya janyo zanga-zanga a Iran bayan da aka kame wata saboda ta cire mayafi tare da rataye shi a icce a bainar jama'a.
An ta yawo da hotunanta a shafukan sada zumunta na intanet a tsaye a bainar jama'a. An sake ta daga bisani bayan an kama ta.
Tun juyin juya halin da aka yi a Iran a 1979, aka tilastawa mata yin shiga ta musulunci.
Source :bbc hausa
Title :
Andaure Wata Mata Saboda Ta Bude Gashinta A Iran
Description : Masu shigar da kara a Iran sun ce an yankewa wata mata hukunci daurin shekara biyu, saboda cire mayafinta da ta yi a bainar jama'a don n...
Rating :
5