Shugaba Donald Trump na kasar Amurka ya rattaba hannu akan dokar da tsohon shugaban kasar ta Amurka Barrack Obama ya saka ta hana daukar mata-maza aikin soja a kasar.
A sanarwar da fadar White House ta fitar ta nuna cewar matakin da shugaban kasar ya dauka ya samu amincewar ministan tsaro na kasar James Mattis. Sannan kuma fadar ta bayyana cewar daga yanzu ta daina daukar duk wadanda keda matsalar al'aura aikin soja.
Fadar ta sanar da cewar ta dauki wannan matakin ne saboda hakan yana haifar da matsala babba a gidan soja, amma fadar ta bayyana cewar akwai yiwuwar a sassauta dokar idan bukatar hakan ta taso.
Bisa dukkan alamu dai shugaba Donald Trump matakin daya dauka yana nuna kalubale ne akan matakin da tsohon shugaban kasar Barrack Obama ya dauka a ranar 1 ga watan Yuli wacce take nuni da bawa mata-maza damar shiga aikin soja a kasar.
Baya da haka shugaba Donald Trump ya kara tabbatar da cewa bayan hana mata-maza shiga aikin na soja, kasar kuma zata daina daukar nauyin wadanda ke canja al'aurar su a asibiti.
Source :naij hausa
Title :
Andaina Daukan Mata-Maza Aikin Soja A Amurka
Description : Shugaba Donald Trump na kasar Amurka ya rattaba hannu akan dokar da tsohon shugaban kasar ta Amurka Barrack Obama ya saka ta hana daukar mat...
Rating :
5