Da sanadin kamfanin dillancin labarai na Najeriya, mun samu rahoton cewa mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo tare da mai dakin sa, Dolapo, uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari, sun halarci liyafar bikin Idris da Fatima Ajimobi.
Kamfanin ya kuma ruwaito cewa, gawurtattun 'yan Najeriya sun yi dandazo a Lambun Agodi dake garin Ibadan na jihar Oyo domin taya wannan ma'aurata murna da madangantan su.
Naij ta ruwaito cewa, an dauran auren Idris, dan gwamna Abiola Ajimobi na jihar Oyo da Fatima, diyar gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano a ranar 3 ga watan Maris a jihar ta Kano wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarta.
Cikin wadanda suka halarci wannan liyafa a garin Ibadan sun hadar da; gwamna Rotimi Akeredelo na jihar Ondo, Rauf Aregbesola na Osun tare da matar sa, Srifat, Ibikunle Amosun na jihar Ogun da kuma Abubakar Bagudu na jihar Jigawa.
Sauran wadanda suka halarci liyafar sun hadar da; Alhaji Aliko Dangote, Janar Yakubu Gowon, Asiwaju Bola Tinubu, Cif Femi Otedola, da sauran ministoci da jiga-jigan gwamnatin kasar nan.
Source :naij hausa
Title :
Anci Gaba Da Bikin Yar Ganduje A Wani Gari
Description : Da sanadin kamfanin dillancin labarai na Najeriya, mun samu rahoton cewa mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo tare da mai dakin sa...
Rating :
5