Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin kasa zagon kasa watau EFCC tayi nasarar damke wani mutumi dauke da makudan Dalolin kudi a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano.
Yanzu haka an soma binciken wannan batu inda aka kama wannan Bawan Allah mai suna Adamu Rabi’u Mohammed dauke da Dala 370, 000. Mohammed na kokarin hawa jirgin Ethiopia domin ya lula zuwa kasar UAE ta Larabawa.
Jami’an Kwastam ne dai su kayi ram da wannan mutumi kamar yadda mu ka samu labari. Yanzu haka dai an mika shi hannun Hukumar EFCC kuma za a maka shi Kotu domin a fara shari’a ba tare da wani bata lokaci ba inji Hukumar.
Dokar kasar dai ta haramta a rika yawo da tsabar kudin da ya haura Dala 10, 000. Kudin da aka kama wannan mutumi da shi sun haura Naira Miliyan 130. Wilson Uwujaren wanda ke magana da yawun EFCC ya bayyana mana wannan.
Source :naij hausa
Title :
Anakama Wani Mutum Da Daloli Na Kokarin Tserewa Daga Nijeriya
Description : Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin kasa zagon kasa watau EFCC tayi nasarar damke wani mutumi dauke da makudan Dalolin kudi a filin ji...
Rating :
5