An yi kira ga tsofaffi a Wales su yi tunani game da bayar da kyautar kwakwalwarsu idan sun mutu don taimakawa masana kimiya da ke bincike a kan cutar mantuwa.
Masu bincike a Jami'ar Cardiff ba su fara dauka ba a yanzu, amma suna fatan samun goyon baya daga mutane da suka haura shekaru 85.
Sannan sun ce kofa a bude ta ke ga masu dauke da cutar a yayin da kuma suke bukatar gudunmuwar kwakwalwar mutane masu lafiya domin gudanar da binciken.
Daya daga cikin wadanda suka bayar da kyautar kwakwalwarsu Ken Bexter mai shekaru 75 ya ce, "Idan na mutu, ba ta da wani amfani gare ni."
Tun a 2009, mutane 460 suka yi rijista, kuma a yanzu 79 sun yi nasarar bayar da gudunmuwar kwakwalwa ga aikin binciken cutar mantuwa.
Ana karbar mutane ne ta hanyar wata kungiya a Jami'ar, da ke aikin tantancewa tare da gano nau'in kwakwalwar da ta dace da masu dauke da cutar.
Ana fatar daga nan za su iya gano mutanen da za su iya cin moriyar taimakon kwakwalwar.
Amma kafin hakan, sai sun yi nazari sosai akan kwakwalwar mutane, tare da diba sinadaran da suka rarrabu a kwakwalwar wanda ake ganin shi ne hanyar da za ta taimaka a gano ainihin cutar.
Ko da yake idan daga cikin masu dauke da cutar suka amince a yi gwajin da su, zai iya kawo cikas wajen janyo hankalin masu lafiyar kwakwalkwar domin su bayar da kyautar kwakwalwar idan sun mutu.
Mista Baxter ya ce ya yanke shawarar bayar da kyautar kwakwalwarsa ne, bayan ya ga yadda abokinsa ke fama da cutar mantuwa.
Yana ganin wannan hanya ce ta taimakawa wasu, amma ya amsa cewa ba kullum ba ne ya ke samun yabo game da matakin da ya dauka ba.
Ya ce, "Mutane na cewa, ka tabbata? Ba abu ba ne da nake son yi". Wasu mutanen kuma suna kidimewa idan ka fada ma su. Ni ban ga dalili ba amma mutane da yawa sun yi wa abun mummunar fahimta.
"Suna tunanin ban taba tunanin haka ba', amma ga shi kana taimakon wani. Idan har za mu iya yakar wannan cutar, ya fi dacewa"
Idan na gama amfani da ita (Kwakwalwata), ba ta da wani amfani kuma a gare ni," a cewarsa.
Kate Baxter ba ta yanke shawarar ko za ta bayar da kyautar kwakwalwarta kamar mijinta ba.
Matar Mista Baxter ra'ayinta ya sha banban, ko da yake ta goyi bayan matakin da mijinta ya dauka.
Ta ce: "Zai ba shi mamaki cewa ni ba zan iya yin haka ba."
"Babu shakka akwai bambanci ka bayar da kyautar koda ko hanta, saboda za a ba wani kuma zai yi amfani da shi.
"Za a iya amfani da kwakwalwar ta wata hanya daban, ba za a yi amfani da ita a kan wani mutum ba kuma a yi tunanin za ta yi aiki a hanyar da ta saba, watakila wannan zai sa mutane su kaurace."
Yadda za ka bayar da kyautar kwakwalwarka
Za ka yi rijista kana raye, Za ka bar wasiya cikin sa'o'i 72 domin karba, amma yawanci ana karanta wasiya kwanaki bayan rasuwa wanda hakan ya nuna lokacin karba ya kure.
Za ka sanar da iyalinka ko dangi, kan shawarar da ka yanke saboda su san me za su yi idan ka mutu.
Daya daga cikin masu binciken Rachel Marshall
Rachel Marshall, jami'ar da ke taimakawa binciken, ta ce a yanzu suna neman mutane masu lafiya da suka haura shekaru 85. "Su muke bukata a yanzu domin aiwatar da gwajin".
Lokacin da aka bayar da kyautar kwakwalwa, za a raba ta biyu rabi za a ajiye a kankara, sauran rabin kuma za a ajiye domin bincike a kai.
Ta ce za a iya ajiye samfurin har abada kuma wadanda aka samu shekaru da dama da suka gabata har yanzu ana amfani da su.
Source :bbc hausa
Title :
Ana Neman Tsofaffin Da Zasu Bada Kyautar Kwakwalensu
Description : An yi kira ga tsofaffi a Wales su yi tunani game da bayar da kyautar kwakwalwarsu idan sun mutu don taimakawa masana kimiya da ke bincike a ...
Rating :
5