Wani dalibi mai shekaru 20, Sultan Bello da ke yi ma Sarkin Kano sojan gona ya gamu da fushin wata kotun majistri dake zamanta a jihar Kano, inda ta bada umarnin garkame shi a gidan Kurkuku.
Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito Alkalin Kotun Hassan Ahmad ne ya bada wannan umarni bayan sauraron laifuka guda uku da ake tuhumar Sultan, mazaunin Ja’oji, da suka hada da sojan gona, cin amana, da kuma bata suna.
Da farin zaman na ranar Laraba 21 ga watan Maris, Dansanda mai shigar da kara Haziel Ledapwa ya bayyana ma Kotun cewar Sultan ya aikata laifukan ne a ranar 27 ga watan Feburairu ta wata shafin Instagram da yake amfani da shi da sunan mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II.
“Ya nemi kimanin kudi Naira miliyan 1.85 daga mutanen da suka hada da; Baraka Sani ta bashi naira miliyan 1.4, N150,000 daga Sadiq Saflan, N50,000 daga Sadiq Sani, N50,000 daga Aisha Ahmad, N50,000 daga Surajo Zakari da kuma N150,000 daga Yahaya.
”Dansanda ya kara da cewa Sultan ya nemi wadannan kudade ne da nufin biyan wata mawakiyar fina finan Hausa mai suna Zubaida Mu’azu da ta yi masa waka, a matsayinsa na Sarkin Kano, inda yace su tura kudaden zuwa asusun banki mai lamba 3049986447, bankin First Bank.
Daga karshe Dansandan yace hakan ya saba ma sashi na 132, 322 da 392 na kundin hukunta manyan laifuka. sai dai a zaman na ranar Laraba, Sultan ya amsa dukkanin laifukan da ake tuhumarsa, bayan nan kuma Alkali y adage sauraron karar zuwa 26 ga wata Maris.
Source :naij hausa
Title :
An Yanke Hukunci Wa Matashin Dake Sojan Gona Wa Sunusi Lamido Sunusi
Description : Wani dalibi mai shekaru 20, Sultan Bello da ke yi ma Sarkin Kano sojan gona ya gamu da fushin wata kotun majistri dake zamanta a jihar Kano,...
Rating :
5