Masarautar Damagaram ta jamhuriyar Nijar ta goya wa takwararta Azbin baya bisa amincewa da kafa dokoki saboda a samu sauki wurin aure a yankin, dokokin sun hada da rage kudin sadaki, da hana yin ankon biki, da rage kayan gara, da kuma rage amfani da ababen hawa a lokacin biki wurin kai amarya.
Sarkin Damagaram, Mai Martaba Alhaji Abubakar Sanda, shi ne ya sanar da hakan a lokacin da ya halarci wani taro na masu ruwa da tsaki, wanda ya hada da 'yan kasuwa da kuma kungiyoyin mata a jihar ta Damagaram, Sarkin ya ce masarautar ta dauki wannan kudurin ne bayan jama'ar garin sun kai masa kukansu akan a sama musu sauki akan al'amuran da suka shafi aure da bikin suna da kuma wasu manyan bidi'oi a yankin jihar.
Sarkin ya ce, sun zauna sun yi nazari sosai akan wannan bukata ta al'ummar, saboda haka yanzu mun saka doka, saboda dukkan abubuwan da jama'ar jihar suka kawo kuka akan su dama addini ya hana yin su.
Haka zalika Mai Martaba Sarkin ya kara da ce, irin wadannan bidi'oin, sukan tilasta wasu zuwa su ciyo bashi domin suyi abinda bai zama dole ba a addini.
A yanzu haka dai, masarautar ta garin Damagaram ta rage kudin sadakin aure daga jaka 50 zuwa jaka 20, sannan kuma masarautar ta hana daukan amarya a cikin jerin gwanon motoci, sannan an rage kayan gara, daga karshe kuma an hana yin ankon biki kwata-kwata a jihar.
Source :naij hausa
Title :
An Rage Kudin Sadaki A Nijar
Description : Masarautar Damagaram ta jamhuriyar Nijar ta goya wa takwararta Azbin baya bisa amincewa da kafa dokoki saboda a samu sauki wurin aure a yank...
Rating :
5