- Jihar Zamfara ta dade tana fama da tashe-tashen hankula a hannun 'yan bindiga da 'yan fashi da kuma barayin shanu
- A cigaba da yaki da aiyukan ta'addanci a jihar, jami'an tsaron farin kaya (DSS) sun hallaka wani gagararren barawon shanu da ake kira 'janar' Buhari-
Haka a kudancin Najeriya, jami'an tsaron sun yi nasarar kama wani gagararren mai garkuwa da mutane, Anthony Kio ElegweKamar yadda ku ka sha karantawa a labaran naij.com, jihar Zamfara ta dade tana fama da tashe-tashen hankula a hannun 'yan bindiga da 'yan fashi da ma barayin shanu.
A cigaba da yaki da aiyukan ta'addanci a jihar, jami'an tsaro sun yi nasarar kashe wani gagararren barawon shanu da ake kira 'janar Buhari' wanda hukumar DSS ta ce sunan sa na gaskiya Umar Abubakar. An kashe shi tare da wani da su ke aikata laifi tare a karamar hukumar Adavi dake jihar Kogi.
A wata sanarwa da hukumar DSS ta fitar bakin Tony Opuiyo, wanda ya yi magana da manema labarai a madadin hukumar, ya ce sun yi nasarar damke wani Isiah Suwe, abokin gagararren mai garkuwa da mutanen, Terwase Awkaza, a jihar Binuwai.
Kazalika hukumar ta ce ta yi nasarar damke wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a kudancin Najeriya da ake kira Anthony Kio Elegwe, mai shekaru 37, dan asalin Oyigba dake karamar hukumar Ahoada ta yamma a jihar Ribas. An kama shi ne a jihar Bayelsa ranar 22 ga watan Fabrairu.
Kazalika hukumar ta a ce ta kama masu aikata laifuka daban-daban tare da kama makamai masu tarin yawa daga hannun 'yan ta'addar a sassan kasar nan.
Source :naij hausa
Title :
An Hallaka Janar Buhari A Zamfara
Description : - Jihar Zamfara ta dade tana fama da tashe-tashen hankula a hannun 'yan bindiga da 'yan fashi da kuma barayin shanu - A cigaba da y...
Rating :
5