Kungiyar da ke ikaririn Musulunci Islamic State (IS) ta wallafa wani bidiyo da ta ce na mayakanta ne lokacin da suka yi wa sojin Amurka hudu kwanton-bauna sannan suka kashe su a Jamhuriyar Nijar a watan Oktoban da ya wuce.
Ba a san takamaimai dalilin da ya sa sai yanzu suka fitar da bidiyon ba - ta manhajar Telegram mallakin kungiyar.
Yawancin bidiyon yana nuna hotunan abubuwan da suka faru ne, ciki har da hotunan da aka dauka ta hanyar amfani da na'urar daukar hoton da ake makalawa a goshi ta daya daga cikin sojojin.
Bidiyon ya nuna cewa da alama mayakan IS ne suka kashe sojojin.
Mutuwar sojojin ta jawo ce-ce-kuce bayan matar daya daga cikin sojojin, Army Sgt La David Johnson, ta ce Shugaba Donald Trump ya sanya ta kuka lokacin da ya buga mata waya domin ya taya ta jaje, inda ya ce mijinta nata ya san idan ya shiga aikin soja zai iya mutuwa.
Mene ne ya faru a cikin bidiyon?
Bidiyon ya fara ne da nuna hotunan mayakan Jamaat Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM) da ke da alaka da al-Qaeda suna yin mubaya'a ga shugaban IS Abu Bakr al-Baghdadi.
A watan Maris din 2017 ne kungiyoyon jihadi na Yammacin Afirka suka kafa kungiyar JNIM, inda da farko suka yi mubaya'a ga al-Qaeda.
Masu sharhi da dama sun yi bayani kan yadda mayakan JNIM suka yi mubaya'a ga IS a watan jiya, amma IS din ba ta sanar da hakan ba sai yanzu.
Mayakan IS na son yin amfani da Telegram saboda yana boye sirrin masu amfani da shi.
Bidiyon mai dauke da hotunan da ke da tayar da hankali ya nuna mayakan IS dauke da manyan makamai inda suke tafiye da kuma gudu a cikin hamada, da alama suna nufar inda za su yi wa sojojin kwanton-bauna, in ji BBC Monitoring.
An ga sojojin suna gudu a wata farar mota, inda hayakin gurneti ke rufa musu baya.
Daga nan ne aka ga sojojin a kusa da wata mota kirar Jeep, inda daya daga cikinsu ke bude wuta yayin da biyu ke tafiya a bayansa suna bude wuta kan wadanda suka kai musu hari.
Bidiyon ya nuna yadda daya daga cikin sojojin ya fadi kasa. Mutumin da ya sanya na'urar daukar hoton da ake makalawa a goshi ya yi kokarin tashinsa.
Sojan da ke tuka motar ya tsallake ya fita daga cikinta sannan ya taimakawa ya janye dan uwansa da ya fadi, kafin su fada hannun mayakan IS.
Amurka ta girke sojoji kimanin 800 a Jamhuriyar Nijar, wadanda ke horas da jami'an tsaron kasar kan yaki da ta'addanci.
Source :bbc hausa
Title :
An Fidda Video Kisan Sojojin Amurka Da Akayi A Nijar
Description : Kungiyar da ke ikaririn Musulunci Islamic State (IS) ta wallafa wani bidiyo da ta ce na mayakanta ne lokacin da suka yi wa sojin Amurka hud...
Rating :
5