Karamin Ministan Man Fetur na Najeriya, Dokta Ibe Kachikwu, ya ce Najeriya ta rasa cinikin dake tsakanin ta da kasar Amurka na danyen man fetur har abada, a matsayin ta na kasar da tafi kowacce siyan danyen mai a Najeriya.
Ya ce har zuwa shekarar 2000, kasar Amurka ita ce kasar da tafi kowacce sayen danyen mai a Najeriya, inda take sayen kimanin ganga 700,000 a kowacce rana, inda a shekarar 2006 kuma ta kara sama daga ganga 700,000 zuwa ganga miliyan 1.31 a rana.
Ya ce tun daga lokacin ana ta samun raguwar sayen danyen man, inda kasar ta tsaya da sayen danyen man a shekarar 2015, bayan ta hada kai da kamfanin samar da mai na shale, inji Kachikwu.
Mista Kachikwu ya kara da cewa yanzu yankin Asiya sune suka fi son danyen man Najeriya din musamman ma kasar India. Ya ce yawan man da Najeriya ta ke fitar wa a kullum ya karu ya kai miliyan 2.07 a watan Fabrairun nan, kamar yadda ma'aikatar man fetur ta kasa ta kiyasta.
Source :naij hausa
Title :
Amurka Ta Daina Sayen Man Fetur A Hanun Nijeriya
Description : Karamin Ministan Man Fetur na Najeriya, Dokta Ibe Kachikwu, ya ce Najeriya ta rasa cinikin dake tsakanin ta da kasar Amurka na danyen man fe...
Rating :
5