Masu iya magana sunce lafiya ce uwar jiki, sannan kuma abu ne da kudi baya iya siyansa.
A zamanin nan da muke ciki cuttutuka sunyi yawa inda ya zama babu babba babu yaro, hakan ne ya sa muka binciko maku wasu magani da ganyen zogale ke yi a jikin dan adam.
Ga wasu daga cikin amfani 18 da zogale ke yi:
1. Da farko zaa dafa ganyen zogale da zuma a sha kamar shayi domin magance gyambon ciki wato ulcer.
2. Duk wanda ke fama da ciwon kai ya nemi ganyen zogale ya shafa a goshinsa.
3. Ganyen zogale na amfani wajen tsayar da jini idan mutun ya yanke.
4. Ana hada zogale da man zaitun domin maganin kurajen jiki.
5. Ana zuba garin zogale a cikin abinci ga mai cutar hawan-jini da neman karin kuzari.
6. Zogale na saurin warkar da rauni ko gyambo.
7. Fure zogale da zuma na kara wa mace ruwan nono a lokacin da take shayarwa.
8. Ana dafa furen zogale da citta domin magance ciwon siga da yawan fitsari.
9. Ga mai ciwon shawara ya nemi zogale da kanwa kadan ya dafa.
10. Diga ruwan zogale na maganin ciwon kunne da ido.
Source :naij hausa
Title :
Amfanin Zogale A Jikin Dan Adam
Description : Masu iya magana sunce lafiya ce uwar jiki, sannan kuma abu ne da kudi baya iya siyansa. A zamanin nan da muke ciki cuttutuka sunyi yawa ind...
Rating :
5