Tsohon gwamnan jihar Jigawa, kuma tsohon minista a gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, Alhaji Sule Lamido ya bayyana dalilin da yasa yake son zama shugaban kasar Najeriya.
Lamido ya bayyana cewar ba kwadayi yasa yake hankoron zama shugaban kasa ba, inda yace muradin bautawa ma yan Najeriya, tare da son gyaran kasar nan yasa yake matukar kaunar zama shugaban kasa.
Kamfanin dillancin labaru NAN, ta ruwaito Lamido ya bayyana haka ne a ranar Alhamis 22 ga watan Maris, a yayin wani taron tattaunawa da yayi da yayan jam’iyyar PDP na jihar Legas, inda ya soki gwamnatin APC, da cewa bata tabuka ma yan Najeriya komai ba, don haka dole su canza ta.
Majiyar naij hausa ta ruwaito Lamidon na fadin jam’iyyar APC ta yaudari yan Najeriya da alkawurran da ta daukan musu a yayin yakin neman zabe, da suka hada da yaki da rashawa, samar tsaro da kuma inganta tattalin arziki.
Sa’annan ya bayyana kansa a matsayin cikakken dan jam’iyyar PDP da ya dace ya zama dan takarar jam’iyyar na takarar shugaban kasa a shekarar 2019, duba da dadewarsa a jam’iyyar da sanin siyasar Najeriya.
Daga karshe yayi kira ga yayan jam’iyyar PDP da su hada kansu don kawar da APC a 2019, “Har sai mu yan PDP mun hada kanmu ne zamu iya kawar da APC a 2019, inda kuma muka yi sake APC ta koma mulki, sai Allah ya tambayemu.” Inji shi.
Source :naij hausa
Title :
Allah Zai Tambayemu Idan Mukayi Sak A 2019 - Sule Lamido
Description : Tsohon gwamnan jihar Jigawa, kuma tsohon minista a gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, Alhaji Sule Lamido ya bayyana dalilin d...
Rating :
5