Shahararriyar jarumar nan da tayi fice a harkar shirya fina-finan Hausa Maryam Both tayi raddi ga masu amfani da sunanta a shafukan yanar gizo.Jarumar tayi Allah ya isa ga masu amfani da sunan nata suna bata mata suna.
Ta kuma ce ita ta san mutuncin dan Adam ballantana malaman addini domin a cewarta ita daga gidan tarbiya ta fito.Har ila yau jarumar tayi Allah ya isa inda tace bazata taba yafewa ba har duniya ta nade.
Kamar yadda kuka sani a makon da ya gabata ne aka zargi jarumar da sukar shugaban kungiyar Hisbah Mallam Aminu Ibrahim Daurawa inda tace yayi rashin adalci da munafurci sakamakon kin magana da yayi akan auren yar gwamnan jihar Kano wato Fatima Ganduje.
An wallafa wannan labari ne da sunan jarumar a shafin Facebook, inda labarin ya bazu.
Source :naij hausa
Title :
Allah Ya Isa Ga Duk Wanda Yayi Amfani Da Sunana A Yanar Gizo Yana batamin Suna - Maryam booth
Description : Shahararriyar jarumar nan da tayi fice a harkar shirya fina-finan Hausa Maryam Both tayi raddi ga masu amfani da sunanta a shafukan yanar gi...
Rating :
5