Wata Kotun majistri dake zamanta a unguwar Gyadi gyadi na jihar Kano ta yanke ma wani dalibin dan aji shida da ba’a bayyana sunansa ba, hukuncin sharan farfajiyar Kotun, inji rahoton Daily Trust.
Dansanda mai kara ya shaida ma Kotun cewa a ranar18 ga watan Feburairu ne wani mutum mai suna Muhammad Sani mazaunin unguwa uku, ya kai kara zuwa ofishin Yansandan cewa yaron ya fasa masa shago inda aka tafka masa sata.
Muhammad Sani ya bayyana ma Kotun cewa Yaron ya sace masa galolin mai guda biyar, sai dai babu komai a cikinsu, amma darajarsu ta kai N3,500 a duk guda, hakazalika dumu dumu aka kama shi da su.
Sa’nnan da aka karanto masa laifukan da ake tuhumarsa da su, sai yaron ya kada baki ya amsa laifukan gaba daya, daga nan sai Alkali Hajara Garba ta yanke masa hukuncin shara, inda ta umarce shi ya share farfajiyar Kotun na tsawon awanni guda 3, daga nan sai ta sallame shi.
Source :naij hausa
Title :
Alkalin Wani Kotu Ya Yan Yanke Ma Wani Yaro Sharan Kotu Na Taswon Awa Uku
Description : Wata Kotun majistri dake zamanta a unguwar Gyadi gyadi na jihar Kano ta yanke ma wani dalibin dan aji shida da ba’a bayyana sunansa ba, huku...
Rating :
5