Dakta Junaid Muhammad, tsohon dan majalisa kuma shahararren dan siyasa ya bayyana cewa, za a yi gagarumin tashin hankali muddin jam'iyyar APC ta yi wani magudin zabe a 2019 da zai taka rawar gani wajen samun nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Ya ke cewa, tuni 'yan Najeriya suka dawo daga rakiyar sa domin kuwa sun gaji da wannan gwamnatin mai mulkin kama karya.
A yayin ganawa ta musamman da manema labarai na kamfanin jaridar This Day a ranar Larabar da ta gabata, gogaggen dan siyasar ya bayyana cewa zai kasance wasan kwaikwayo matukar aka sake zaben shugaba Buhari a shekara mai gabatowa.
Yake cewa, "cikin rashin ra'ayin al'ummar kasa da ma'aunin hankali gami da rashin gaskiya ga shugaba Buhari ya sake tsayawa takara kuma ya samu magoya tamkar yadda ya sa mu a garin Kano, domin kuwa a halin yanzu ba bu ko abu guda na nunawa da ya yiwa kasar nan.
"Junaid ya ci gaba da cewa, a sakamakon yadda rashin tsaro, katutu na talauci da kuma ta'azzara ta rashawa a kasar nan, shugaba Buhari bai cancanci ya sake neman takara ba.
Ya kara da cewa, Buhari shugaba ne da wani rukunin mutane jagoranta ta yadda aka tsare-tsaren sa na yaki rashawa domin 'yan uwan sa da abokai su wadata.
Source :naij hausa
Title :
Akwai Tashin Hankali Idan APC Tayi Magudin Zabe - Dr. Junaid
Description : Dakta Junaid Muhammad, tsohon dan majalisa kuma shahararren dan siyasa ya bayyana cewa, za a yi gagarumin tashin hankali muddin jam'iyya...
Rating :
5