A halin yanzu dai Najeriya ta yi asarar sama da Naira miliyan dubu 2.6 wajen kawar da gudanarwa tawaye da ta'addancin 'yan Boko Haram a yankin Arewa Maso Gabashin kasar nan kamar yadda shugaban hafsin sojin kasa ya bayyana, Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai.
A yayin wakilcin shugaban hafsin sojin a wata lacca kan bincike da nazarin ci gaba da aka gudanar a jami'ar Ahmadu Bello dake garin Zaria a ranar Juma'ar da ta gabata, Manjo Janar Nuhu Ambazo ya bayyana cewa wannan shine adadin dukiya da kadarori da 'yan ta'addan suka salwantar.
Yake cewa, ya kamata a inganta amfanuwa da albarkatu da ma'adanan Najeriya wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, sai dai tawaye daban-daban ya maishe da kasar wani dan karamin filin yaki da ake fafata yakoki na siyasa, kalibalanci da kuma rikicin addini.
A na sa jawabin shugaban jami'ar ABU, Farfesa Ibrahim Garba ya bayyana wannan taro a matsayin wani ɓangare na gudanar da harkokin ilimi a jami'ar.
Jaridar Naij kuma ruwaito cewa, a ranar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika da sakon gaisuwar ga al'umma da gwamnatin jihar Edo dangane da rashin surukin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.
Source :naij hausa
Title :
Adadin Kudaden Da Aka Kashe Don Yakan Yan Tawaye - Buratai
Description : A halin yanzu dai Najeriya ta yi asarar sama da Naira miliyan dubu 2.6 wajen kawar da gudanarwa tawaye da ta'addancin 'yan Boko Hara...
Rating :
5