Kungiyar makiyaya na Miyetti Allah ta Najeriya ta yi jinjina bisa ga ziyarar da shugaba Buhari ya kai a Jihar na Taraba. Ciyaman din na Arewa maso Gabashin kasa na kungiyar, Alhaji Mafindi Umar, yace ziyarar shugaban kasar zai bunkasa zaman lafiya a tsakanin mutanen Jihar.
Ya kuma yi kira da a gudanar da bincike don ganowa da hukunta wadanda aka samu da hannu a kisar tsibirin Mambilla kamar yadda jaridar Daily Post ta ruwaito.
"Ziyarar ta bamu damar fada wa shugaban kasa abubuwan da muke fuskanta, wanda muna fatan da an shirya tsakanin kabilu na jihar za’a samu zaman lafiya.
"Tura Sojoji da Yan Sanda ba shine zai gyara al’amarin ba, amma idan akwai gaskia da adalci, to za’a magance matsalar," inji shi.Bayan haka, Gwamnatin Jihar ta ce, ziyarar tana kara nuna jajir cewar shugaban kasa kan samar da dorariyar zaman lafiya da magance kasha-kashe.
Babban mai taimakawa Gwamna ta fannin sadarwa da jama’a, Mr Bala Dan-Abu, yace ziyarar ta ba wa shugaban kasa damar saurare daga bakin jama’a, Duk da dai wannan shine karo na farko da shugaban kasar yayi jawabi a kan kisan da akeyi a jihar ta Taraba.
"Gwamnatin Jihar Taraba sunji dadin cewar ba wai shugaban kasar ba wai kawai yazo don a ganshi ba ne kadai, amma don samar da mafita ga matsalar da ake fuskan ta," inji shi.
Source :naij hausa
Title :
Abunda Yan Miyetti Allah Suka Fadawa Buhari Yayin Ziyartar Shi Taraba
Description : Kungiyar makiyaya na Miyetti Allah ta Najeriya ta yi jinjina bisa ga ziyarar da shugaba Buhari ya kai a Jihar na Taraba. Ciyaman din na Arew...
Rating :
5