Sanata Shehu Sani, mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya a majalisan dattawan tarayya ya bayyanawa duniya cewa shi da abokan aikinsa kan amshi N13.5 million a wata domin ayyukan jin dadinsu sabanin albashin da suke samu.
A wata hira da yayi da BBC, Shehu Sani ya bayyana dalilin da ya sa yayi hakan.Yace: “Na yanke shawaran bayyanawa ne saboda kare mutunci,”Ya ce ana gudanar da majalisan dokokin tarayya cikin rashin gaskiya kan yadda aka kasha kudade.Yana son a daina biyan Sanatoci kudin Haram saboda maras aikinyi su daina takara zaben majalisa kowani shekaran zabe.
“Majalisan dokokin tarayya na daga cikin ma’aikatun gwamnati da rashin gaskiya yafi yawa. Na duba al’amarin sai nay a kamata in bayyanawa duniya kowa ya gani.
”Sanata Shehu Sani ya yi bayani a wata hira da jaridar The News cewa suna karban N13.5 million a wata sabanin N750, 000 kudin albashi sannan wasu alawus.
Source :naij hausa
Title :
Abinda Yasa Na Baiyana Albashin Sanatoci-Shehu Sani
Description : Sanata Shehu Sani, mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya a majalisan dattawan tarayya ya bayyanawa duniya cewa shi da abokan aikinsa kan am...
Rating :
5