A ranar Laraba 21 ga watan Maris ne wasu mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram suka mayar da wasu daga cikin yan mata 110 dalibai sakandarin kimiyya na garin Dapchi dake jihar Yobe bayan kwashe kimanin wata guda a hannunsu.
Sai dai wasu rahotanni da jaridar naij ta samu sun tabbatar da cewar yan ta’addan sun ki sakin wata dalibar kwalejin mai suna Leah Sharibu, Kirista daya tilo dake cikin yan matan, saboda wai ta ki yarda ta sauya addininta daga Kiristanci zuwa Musulunci.
Labarin wannaan yarinya ya watsu a shafukan sadarwa da dama, wanda hakan ya janyo cece kuce a tsakanin mabiya shafukan, inda mahaifiyarta da mahaifinta suka ce suna alfahari da wannan diyar tasu, saboda riko da addininta.
Sai dai a wata hira da yayi da BBC Hausa, shugaban kungiyar Izala, Sheikh Bala Lau ya mayar da martani game da wannan, inda yace yan ta’addan Boko Haram basa wakiltar Musulman Najeriya, ya kara da cewa karara sun yi hannun riga da musulunci.
Source :naij hausa
Title :
Abinda Boko Haram Sukeyi Yafita A Musuluncin - Bala Lau
Description : A ranar Laraba 21 ga watan Maris ne wasu mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram suka mayar da wasu daga cikin yan mata 110 dalibai sakand...
Rating :
5